Eno ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a wani taro a gidan gwamnatin jihar da ya samu halartar gwamnonin jihohin Legas, Ogun, Edo, Delta, Ebonyi da Cross River.
Ya ce da safiyar ranar ya mika takardar ficewa daga jam’iyyar PDP ga shugaban jam’iyyar na mazabarsa, an kuma aika kwafin guda ga shugabannin jam’iyyar na jiha da na kasa.
