Monday, April 6, 2026
HomeSiyasaGwamnan jihar Ogun ya nada mataimaka 1200 

Gwamnan jihar Ogun ya nada mataimaka 1200 

Gwamnatin Ogun karkashin jagorancin gwamna Dapo Abiodun ta nada mutane 1200 domin taimaka mata wajen kawo sauyi a jihar.

Cikin wata sanarwa da gwamnan ya fitar ta hannun mataimakinsa Kayode Akinmade, ya ce wannan yunkuri ne na gwamnatinsa wajen ganin ta yi tafiya da kowane dan jihar a tsari irin na dimukuradiyya.

An zabo mataimaka biyar daga kowace mazaba cikin 236 da ake da su a fadin jihar, kamar yadda Channels TV ya wallafa.

Gwamnan ya bukaci mataimakan nasa su kasance masu bayar da kowacce irin gudunmawa wajen ganin an ciyar da jihar ta Ogun gaba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata