Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya kaddamar da kwamitin mutane 14 domin nazarin batun kafa ‘yan sandan jiha a jihar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa matakin ya biyo bayan umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ga jihohi na su fara shirye-shiryen kafa ‘yan sandan jiha.
Gwamnan ya ce kwamitin zai yi cikakken nazari kan yadda tsarin ‘yan sandan jiha zai dace da tsarin tarayyar Nijeriya, tare da gabatar da shawarwari da za su taimaka wajen tsara manufofin tsaro a matakin kasa.
Shugaban kwamitin, tsohon DIG Habila Joshak, ya ce za su gudanar da aikinsu da gaskiya domin taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar.
