Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya amince da nadin jami’ai 34 tun daga kwamitoci, hukumomi, da mukaman shawara daban-daban a fadin jihar domin inganta gudanar da gwamnati da kuma karfafa ayyukan jama’a.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Ibraheem Musa, ya fitar a ranar Lahadi, an bayyana cewa nadin na da nufin bai wa kwararru masu hazaka da kwarewa damar ba da gudummawa ga cigaban tattalin arziki da siyasar jihar.
Daga cikin sabbin nade-naden akwai Dr. Suwaiba Shehu Ibrahim, da aka nada a matsayin shugabar hukumar Ilimin sakandare ta jihar Kaduna, ta taba zama sakatariyar dindindin a hukumar koyar da malamai ta jihar, kuma malama ce a Jami’ar Kaduna.
Sauran mambobin sun hada da Nita Byack George, Monday Tela Bako, Aliyu Haruna Ahmed, da Hon. Aliyu Ibrahim, yayin da Muhammad Kabir Uthman, lauya kuma masani a fannin gudanarwa, ya zama sakataren hukumar.
