Wednesday, April 8, 2026
HomeLabaraiGwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya rantsar da sabon shugaban hukumar yaki...

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya rantsar da sabon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar “Anti Corruption”

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya rantsar da Barrister Sa’idu Yahaya a matsayin sabon shugaban hukumar karɓar korafe-ƙorafe da yaƙi da cin hanci ta jihar Kano PCACC.

An gudanar da rantsuwar ne a gidan gwamnatin Kano, karkashin jagorancin kwamishinan shari’a na jihar, Barrister Haruna Isa Dederi.

Tun da farko, Gwamnan Kanon ya miƙa sunan Barrister Sa’idu Yahya ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatarwa a matsayin sabon shugaban hukumar.

Barrister Sa’idu Yahaya ƙwararren masani ne a fannin yaƙi da cin hanci, inda ya shafe sama da shekaru 18 yana aiki a hukumar ICPC, musamman wajen bincike da bin diddigin kadarori.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata