Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya amince da korar mataimaka biyu bayan rahoton kwamitocin bincike ya tabbatar da laifukansu.
An kori Abubakar Umar Sharada, SSA kan wayar da kan siyasa, bayan an tabbatar da hannunsu wajen ba da belin wani babban dillalin miyagun kwayoyi, Sulaiman Aminu Danwawu.
Haka kuma, an salami Tasiu Adamu Al’amin Roba, SSA a ofishin majalisa, bayan kama shi yana sake shiryawa da karkatar da hatsi na tallafin palliative da gwamnati ta raba a shekarar 2024.
Tuni sanarwar ta ce an umarnci tsoffin hadiman su mika duk kadarorin Gwamnati da ke hannunsu kafin Litinin, 11 ga Agusta, tare da gargadin kada su sake yi wa kansu lakabin jami’in Gwamnati.
A gefe guda, an wanke Hon. Musa Ado Tsamiya, mai ba da shawara kan magudanar ruwa, bayan kwamitin bincike ya tabbatar da Rashin laifinsa.
