Tuesday, April 7, 2026
HomeLabaraiGwamnan Katsina ya nada sabon shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin jihar

Gwamnan Katsina ya nada sabon shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar

Gwamnan jihar Katsina ya amince da nadin Hon Abdulƙadir Mamman Nasir a matsayin sabon shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar.
Abdulƙadir Mamman Nasir ya maye gurbin Hon Jabiru Abdullahi Tsauri wanda Shugaba Tinubu ya nada mukami a Abuja.
Kafin nadin na Hon Abdulƙadir, shi ne shugaban hukumar kula da nomar rani ta jihar Katsina wato Katsina Irrigation Authority.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun Gwamnan Malam Ibrahim Kaulah Mohammed da DCL Hausa ta samu kwafi a Katsina.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata