Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiGwamnan Kebbi Nasir Idris ya dakatar da Kwamishinan Lafiya saboda sakaci a...

Gwamnan Kebbi Nasir Idris ya dakatar da Kwamishinan Lafiya saboda sakaci a bakin aiki

Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayar da umarnin dakatar da Kwamishinan Lafiya na jihar, Kwamared Yunusa Isma’il, daga mukaminsa nan take har zuwa wani lokaci.

Sanarwar da Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Yakubu Bala Tafida, ya fitar a yau Alhamis a Birnin Kebbi, ta bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne bisa zargin sakaci da yin watsi da aikinsa.

A cewar sanarwar, Gwamna Idris ya umarci Kwamishinan da aka dakatar ya bayar da cikakken bayani kan dalilin da zai sa kada a ɗauki matakin ladabtarwa a kansa.

Hakan, a cewar gwamnatin jihar, ya biyo bayan raina aikinsa da kuma rashin mutunta amanar da aka ɗora masa a matsayin Kwamishinan Lafiya.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata