Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiGwamnan Zamfara ya naɗa Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello a matsayin sabon Sarkin...

Gwamnan Zamfara ya naɗa Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello a matsayin sabon Sarkin Katsinan Gusau

Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya amince da nadin Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello a matsayin Sarki na 16 na Masarautar Gusau, wanda ya gaji mahaifinsa, Marigayi Dr. Ibrahim Bello, da ya rasu a ranar 25 ga Yuli bayan shekaru goma yana sarauta.

A cewar wata sanarwa da ofishin sakataren gwamnatin jihar ya fitar, nadin ya biyo bayan shawarwarin masu zaben sarki na masarautar Gusau, tare da bin al’adun gargajiya da dokoki na kasa.

Alhaji Abdulkadir, wanda shi ne babban ɗan marigayim, yana rike da sarautar Bunun Gusau kafin wannan nadin.

Shi ɗan asalin Malam Sambo Dan Ashafa ne.

Gwamna Dauda Lawal ya taya sabon sarki murna tare da kira gare shi da ya ci gaba da gadon kyakkyawar rayuwa da dabi’un sarakunan da suka gabata, wanda zai zama jigo wajen ɗorewar zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba a masarautar Gusau da kewaye.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata