Tuesday, April 7, 2026
HomeLabaraiGwamnati Nijeriya ta ce ba ta bukatar sojojin haya don shawo kan...

Gwamnati Nijeriya ta ce ba ta bukatar sojojin haya don shawo kan matsalar tsaro

Ministan harkokin waje na Nijeriya Yusuf Tuggar ya ce kasar ba ta bukatar kawo sojojin haya a cikin kasar domin shawo kan matsalar tsaro.
Ministan ya bayyana hakan ne a lokacin wani taron ‘yan jarida na hadin gwuiwa da takwaransa na kasar China Wang Yi, wanda ya kawo ziyara a Nijeriya.
Tuggar ya ce a bayyane take irin yadda Nijeriya ke jagoranci wajen magance matsalolin tsaro tare da tabbatar da zaman lafiya a wasu kasashen saboda da haka ba ta bukatar dauko sojin haya don magance matsalarta.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata