Ta leko ta koma shi ne abin da wasu ma’aikata suka shaida
sakamakon sauyin gwamnati da aka samu jihar Sokoto. A cikin kasa da sa’o’I 24
da tsohon gwamna Tambuwal na jam’iyyar PDP ya mika mulki ne dai, sabuwar
gwamnatin jihar ƙarƙashin jãgorancin
gwamna Ahmad Sule na jam’iyyar APC ta ɗauki matakin sõke daukar ma’aikata da ƙãrin girma da
gwamnatin Aminu Waziri Tambawal ta yi, lamarin da ya sanya da dãma daga cikin
waɗanda aka ɗauka aikin cikin halin ni ƴãsu. Daya daga cikin mutanen da tsohon
gwamna Tambuwal ya dauka aiki a jihar ya shaida wa DCL Hausa yadda suka ji da
kamun ludayin sabuwar gwamnmatinwacce ya zarga da jefa rayuwarsa cikin kunci.
Ita dai sabuwar gwamnatin ta ce irin wadannan ayyuka da
tsohon gwamnan PDP Tambuwal ya rarraba wa mutanen da ta kira “shafaffu da mai”
abu ne da aka yi cikin kuskure wanda ba za ta lamunta ba, a don haka ne ta ce
duk wani karin girma ko daukar aiki da Tambuwal ya yi bayan zaben gwamnan jihar
daga ranar 19 ga watan Maris zuwa na ranar da aka mika mata mulki to ta warware
shi. Sai dai kakakin PDP a jihar ta Sakkwato Hassan Sahabi Sanyinnawal yace
abin da sabuwar gwamnatin jihar ta yi bīta da ƙulli na siyasa ne kawai.
Duk ƙoƙarin da nayi, har tsawon kwanaki biyu, dan jin ta
bakin ɓangaren sabuwar gwamnatin ta jihar Sakkwato, dan jin dalilin soke daukar
aiki da kuma ƙarin girma ga wasu ma’aikata yaci tura.
Wani mai sharhi kan lamurran siyasa, Dakta Umar Adamu na
jami’ar jihar Gombe yace, irin wannan mataki kan iya haddasa gãba a tsakaninin
alumma.
Da alama dai irin
wannan fashin baki da tirjiyar da sabbin am’aikatan da aka dauka ke nunawa ba
za su sanya sabuwar gwamnatin ta jam’iyyar APC dawo da ma’aiaktan na Sokoto
bakin aiki ba, inda baya ga korar wadannan malamai, sabon gwamna Ahmed Sule ya
umurci a soke sababbin sunayen da tsohon gwamna Tambuwal ya rada wa wasu manyan
makarantun jihar.
DCL Hausa, Umar Ibrahim
