Wednesday, April 8, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Bauchi za ta rufe cibiyoyin kiwon lafiya yayin zanga-zangar gama gari

Gwamnatin Bauchi za ta rufe cibiyoyin kiwon lafiya yayin zanga-zangar gama gari

Gwamnatin jihar Bauchi ta bayyana aniyarta na rufe dukkanin cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko a ranar da za a gudanar da zanga-zangar kin jinin gwamnati a fadin kasarnan.

Shugaban Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko na Jihar, Dokta Rilwanu Mohammed yace, an yanke wannan shawarar ne domin barazanar tsaro, kare rayukan ma’aikatan kiwon lafiya da marasa lafiya.

Ya bayyana hakan ne a wajen bude taron manema labarai na shekara biyu kan dabarun bayar da rahoton hidimomin kula da lafiya a matakin farko da aka gudanar a Bauchi ranar Talata.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata