Sunday, April 5, 2026
HomeSiyasaGwamnatin jihar Benue ta musanta batun ficewar gwamnan jihar daga APC

Gwamnatin jihar Benue ta musanta batun ficewar gwamnan jihar daga APC

Gwamnatin jihar Binuwai ta yi watsi da wani rahoto da wata kafar yada labarai ta wallafa na cewa Gwamnan jihar Hyacinth Alia na shirin ficewa daga jam’iyyar APC bisa rikicin da ya barke a jam’iyyar reshen jihar.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, sakataren yada labaran gwamnan, Tersoo Kula, ya ce labarin ba gaskiya ba ne,ya ce a daidai lokacin da gwamnonin jam’iyyun adawa ke komawa APC, saboda manufofi da kuma tsari na jam’iyyar a karkashin shugaban kasa Bola Tinubu, abin dariya ne ace yana yunkurin komawa wata jam’iyyar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata