Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiGwamna Makinde ya tallafa wa ma'aikatan Oyo da ragunan layya a farashi mai rahusa

Gwamna Makinde ya tallafa wa ma’aikatan Oyo da ragunan layya a farashi mai rahusa

Gwamnatin Jihar Oyo ta raba kayan abinci ga ma’aikatan jihar 2,500, da aka sayar cikin sauki domin saukaka musu yin shagulgulan sallar layya ta shekarar 2025.

Shugaban kamfanin bayar da lamunin noma na jihar, Taofeek Akeugbagold ne ya yi raba kayayyakin a harabar kamfanin da ke a Ibadan, babban birnin jihar Oyo a ranar Asabar.

Taofeek Akeugbagold yace kayayyakin sun hada da raguna, buhunan shinkafa, man girki, da sauran kayan abinci, kuma fiye da ma’aikata 5000 sun amfana da wannan tsarin zuwa yanzu.

Ya bayyana cewa shirin wani bangare na kokarin Gwamna Seyi Makinde na inganta jin dadin ma’aikatan gwamnatin jihar, musamman a lokucin bukukuwan sallah.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata