Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Kaduna ta yi watsi da ikiranin da El-Rufai ya yi kan...

Gwamnatin Kaduna ta yi watsi da ikiranin da El-Rufai ya yi kan ayyukan da Tinubu ya kaddamar cewa shi ne ya fara su

Gwamnatin jihar Kaduna ta yi watsi da ikirarin da wani tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai ya yi na cewa dukkanin ayyukan da shugaban kasa Bola Tinubu ya kaddamar a jihar kwanan nan an fara su ne a gwamnatinsa.

El-Rufai, wanda ya mulki Kaduna daga 2015 zuwa 2023, a wata hira da manema labarai a ranar Litinin ya bayyana cewa ayyukan da shugaba Tinubu ya kaddamar a ranar Alhamis din da ta gabata, aikinsa ne

Sai dai kuma a wani martani da ya mayar, babban sakataren yada labarai na gwamna Uba Sani, Ibraheem Musa ya bayyana ikirarin tsohon gwamnan a matsayin karya ce tsantsa da kuma yunkurin canza tunanin mutane.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, ya bayyana cewa ayyukan da ake magana a kai an fara su ne kuma an kammala su a karkashin gwamnati mai ci.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata