Hukumar Gudanar da Asibitoci ta Jihar Kano ta tabbatar da cewa rashin kulawa ne ya janyo mutuwar Aishatu Umar, mahaifiya mai yara biyar, a Cibiyar Abubakar Imam ta Urology, bayan an bar almakashi a cikin jikinta bayan tiyata.
Hukumar ta dakatar da ma’aikata uku da suka shafi lamarin daga aiki, sannan ta mika batun ga Kwamitin Kula da Ka’idojin Likitoci na Jihar Kano don bincike da hukunci.
Iyalan marigayiyar sun nuna bakin ciki, yayin da mutane da dama a shafukan sada zumunta suka nemi a hukunta wadanda suka yi sakaci da kuma yin gyara a harkar lafiya.
Hukumar ta yi ta’aziyya ga iyalan marigayiya tare da tabbatar wa jama’a cewa irin wannan sakaci ba za a lamunta ba.
