Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Kano ta nemi gwamnatin tarayya ta biya ta diyya kan soke...

Gwamnatin Kano ta nemi gwamnatin tarayya ta biya ta diyya kan soke bikin hawan sallah

Gwamnatin jihar Kano ta nemi gwamnatin tarayya ta biya diyya sakamakon soke bukukuwan hawan sallah da aka yi a jere tsawon shekaru biyu.

Kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na jihar, Alhaji Tajo Uthman, ne ya bayyana hakan a lokacin da Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi II, ya kai gaisuwar Sallah ga Gwamna Abba Kabir Yusuf a fadar gwamnatin jihar.

Uthman ya ce jihar ta yi asarar kudade masu yawa saboda dakatar da wannan biki na al’ada da ake gudanarwa a kowace shekara, wanda ke jan hankalin masu yawon bude ido na cikin gida da na kasashen waje.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata