Tuesday, April 7, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Katsina ta bukaci WAEC ta soke jarrabawar turanci da daliban jihar...

Gwamnatin Katsina ta bukaci WAEC ta soke jarrabawar turanci da daliban jihar suka rubuta bana

Gwamnatin Jihar Katsina ta nemi a soke jarrabawar harshen Turanci da Hukumar WAEC ta gudanar kwanan nan, sakamakon jinkirin da aka samu a fara jarrabawar a fadin kasa.

Kwamishinar Ilimi na Firamare da Sakandare, Hajiya Zainab Musa-Musawa, ta bayyana matsayar gwamnatin ne yayin ziyararta ofishin WAEC da ke Katsina, inda ta ce an gabatar da koke a hukumance da sa hannun Babbar Sakatariyar Ma’aikatar, Hajiya Ummukhair Ahmed.

Rahoton kamfanin dillancin labaran Nijeriya ya bayyana cewa WAEC ta danganta jinkirin da kokarin dakile satar amsa ne.
Musa-Musawa ta bukaci iyaye, makarantu da al’umma su kasance masu hakuri har sai an kammala bincike kan batun.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata