Mai ba shugaban Nijeriya shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya bayyana cewa an kashe ‘yan ta’adda da masu aikata laifuka 13,543 a fadin Najeriya tun daga Mayu 2023.
Da yake jawabi a taron APC a Abuja, Ribadu ya ce dakarun soja da hukumomin leken asiri na ci gaba da samun nasara a yaki da ta’addanci.
Ya kara da cewa sama da mayakan Boko Haram da ISWAP 124,408 da iyalansu sun mika wuya, kuma suna cikin shirin gwamnati na sauya tunani da sake shigar da su cikin al’umma kamar yadda jaridar Punch ta ambato.
