Monday, April 6, 2026
HomeKetareGwamnatin mulkin sojin Burkina Faso ta amincewa 'yan Afirka shiga kasar ba...

Gwamnatin mulkin sojin Burkina Faso ta amincewa ‘yan Afirka shiga kasar ba tare da biza ba

Gwamnatin mulkin sojin Burkina Faso ta sanar da bude iyakokin kasar ga dukkan ‘yan Afrika ba tare da biza ba, domin karfafa zirga-zirgar mutane da kuma huldar kasuwanci a kasar.

Sai dai ta ce duk da wannan sassaucin, ga duk wanda keson shiga kasar daga kasashen Afrika za su ci gaba da cike takardar neman izini ta yanar gizo kafin shiga.

Wannan mataki ya sanya Burkina Faso cikin jerin kasashen da suka hada da Ghana, Rwanda da Kenya, wadanda suka sassauta matakai wajen shiga kasashen ga daukacin ‘yan Afrika.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata