Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Najeriya ta ware kusan Naira biliyan 200 don ayyukan jiragen kasa...

Gwamnatin Najeriya ta ware kusan Naira biliyan 200 don ayyukan jiragen kasa a Kano da Kaduna

Gwamnatin Najeriya ta ware kusan Naira biliyan 200 domin aikin samar da jiragen kasa masu zirga-zirga a cikin biranen Kano da Kaduna.

Ministan yada labarai da wayar da kai Alhaji Mohammed Idris ne ya bayyana haka, yayin wani taron manema labarai a Abuja.

A cewar ministan, gwamnatin shugaba Tinubu ta mayar da hankali wajen ganin ta samar da ayyukan ci-gaba a dukkanin matakai, kamar yadda jaridar punch ta ruwaito.

Haka kuma ya ce gwamnatin na kokarin ganin ba a bar kowane bangare a baya wajen samun muhimman ayyukan ci-gaba ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata