Tuesday, April 7, 2026
HomeKetareGwamnatin Nijar ta haramta zanga-zangar neman a saki Bazoum bayan shekaru biyu...

Gwamnatin Nijar ta haramta zanga-zangar neman a saki Bazoum bayan shekaru biyu da juyin mulki

Hukumomin birnin Yamai sun dauki matakin hana zanga zangar lumana da kungiyar farar hula ta MINNJE ta kuduri aniyar yi, domin nuna bukatar a sako tsohon shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum

A cikin wata takarda mai dauke da sa hannun  magajin garin birnin Yamai Kanal Boubacar Soumana Garanké,  hukumomin sun ce sun hana gudanar da zanga zangar ne saboda dalilai na tsaro

A ranar 21 ga watan nan ne dai kungiyar ta Mouvement Indépendant pour un Niger Nouveau dans la Justice et l’Egalité, ko kuma MINNJE a takaice, ta aike wa magajin garin birnin Yaman takardar bukatar gudanar da zanga-zangar lumanar.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata