Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Nijeriya ta amince da sake buɗe bodar  Tsamiya da ke jihar...

Gwamnatin Nijeriya ta amince da sake buɗe bodar  Tsamiya da ke jihar Kebbi domin haɓɓaka kasuwanci

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta amince da sake buɗe iyakar ƙasa ta Tsamiya da ke jihar Kebbi domin ci gaba da kasuwancin ƙetare iyaka, tare da sanya tsauraran matakan tsaro da bin ƙa’idoji.

Kwanturola-Janar na Hukumar Kwastam ta Nijeriya (NCS), CG Adewale Adeniyi, ne ya bayyana hakan a ranar Asabar yayin wata ganawa da masu ruwa da tsaki a jihar Kebbi, ciki har da ’yan kasuwa, masu safarar kaya da kuma ’yan kasuwar albasa.

Adeniyi ya ce matakin sake buɗe iyakar ya biyo bayan umarnin Gwamnatin Tarayya, inda ya jaddada cewa za a gudanar da kasuwancin ne cikin kulawa ta musamman domin tabbatar da tsaro da bin dokokin kwastam.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata