Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Nijeriya ta ce ba ta taɓa sanya hannu kan wata yarjejeniya...

Gwamnatin Nijeriya ta ce ba ta taɓa sanya hannu kan wata yarjejeniya da ASUU ba

Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ba ta da wata yarjejeniya ta doka da ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa, ASUU, sai dai takardun da ke hannun ƙungiyar daftari ne kawai.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa Dr. Alausa ya yi wannan bayani ne a Abuja ranar Alhamis, yayin da yake amsa tambayoyin ’yan jarida kan zanga-zangar da ASUU ke gudanarwa a sassan ƙasar.

Ya ce gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu tana da cikakken niyyar magance matsalolin da suka jima suna jawo rikici tsakanin gwamnati da ASUU tun daga yarjejeniyar 2009 zuwa ta 2021, amma wannan karon za a yi shi ne ta hanya mai dorewa da doka ta amince da shi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata