Ministan ci-gaban harkokin matasa, Mr Ayodele Olawande ya gargadi matasa game da yin kaura ta barauniyar hanya inda ya bayyana irin hadurran da ke ciki.
Olawande ya yi gargadin ne a wani taron gangami da wayar da kan matasa kan illolin bin hanyoyin da ba su kamata ba wajen yin kaura.
Ministan wanda ya samu wakilcin Daraktar da ke kula da kaura da sauyin yanayi, Mrs Grace Lelea a garin Abeokuta ta ce, yin kaura ta hanyar da doka ta shar’anta ba laifi ba ne kuma yana cikin ci-gaban al’umma.
Sai dai kuma, akasin haka da kuma saba wa dokar kasa, cike yake da hadari ga rayuwar al’umma da kuma ci-gaban kasa.
