Gwamnatin Nijeriya ta ƙaddamar da cibiyar kula da na’urorin CCTV da ta lakume biliyan 40 a kan gadar Third Mainland da ke birnin Legas, domin ƙarfafa tsaro da kuma rage yawan haɗurra a gadar.
An ƙaddamar da cibiyar ne a ranar Lahadi, inda ministan ayyuka, David Umahi, ya bayyana cewa aikin ya biyo bayan gyare-gyaren manyan gine-gine da aka yi wa gadar tun bayan da gwamnatin Tinubu ta hau mulki a 2023.
Ya ce an fara sanar da shirin ne tun 2025, kuma za a rika sa ido kai tsaye daga cibiyar tare da tilasta bin ƙa’idar gudun wuce sa a ga masu ababen hawa.
