Gwamnatin Nijeriya ta bai wa sojoji da tsofaffin hafsoshin Rundunar Sojan Nijeriya lambar yabo ta kasa saboda jajircewa, sadaukarwa, jagoranci da hidima ga kasa, ciki har da Brigediya Janar Musa Uba wanda ‘yan ta’adda suka hallaka a Borno.
An gabatar da lambobin yabon ne a bikin tunawa da ranar sojoji ta 2026 a dakin taro na Banquet na Fadar Gwamnatin Nijeriya a Abuja, inda Shugaban Sojan Kasa, Laftana Janar Waidi Shaibu, ya samu lambar Service and Sacrifice.
Brigediya Janar Uba ya samu Gallantry Award saboda nuna jarumta ta musamman da jagorantar sojoji a gaban fagen fama yayin yaki da ‘yan ta’adda a Borno, yayin da Brigediya Janar Usman Ahmad ya samu Mission Success Award kan rawar da ya taka wajen dakile hare-haren ‘yan ta’adda.
An kuma karrama wasu manyan hafsoshin soja, ciki har da tsohon shugaban sojin kasa, Laftana Janar Tukur Yusuf Buratai (rtd.) da tsofaffin sojoji kan gudummawarsu, yayin da Shugaba Bola Tinubu, ta bakin Ministan labarai da, Mohammed Idris, ya shawarci rundunar soja ta cigaba da kasancewa masu ladabi, aminci da hadin kai wajen kare dimokuradiyya.
