Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa za ta sake buɗe dukkan makarantun da aka rufe a Nijeriya sakamakon hare-haren ’yan ta’adda da sace ɗalibai.
Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ne ya sanar da hakan a Minna yayin tarbar ɗalibai 130 da malamansu da aka ceto daga makarantar St. Mary’s da ke Agwara, Jihar Neja.
Shugaban ƙasar, ta bakin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro, Nuhu Ribadu, ya ce an samu nasarar ceto su ne ta hanyar haɗin gwiwar sojoji, ’yan sanda da DSS, yana mai jaddada cewa gwamnati za ta ɗauki matakan tsaro na gaggawa tare da haɗa shugabannin al’umma domin kare makarantu da rayukan jama’a.
A nasa ɓangaren, Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Bago, ya nuna godiya ga Shugaban ƙasa, mai ba shi shawara kan tsaro da hukumomin tsaro bisa nasarar ceto dukkan ɗalibai da malamansu lafiya, yana mai cewa wannan nasara ta musamman ce wadda za ta ba iyaye da al’umma kwarin gwiwa.
