Gwamnatin Nijeriya ta yi Allah-wadai da juyin mulkin da sojoji suka yi a Guinea-Bissau, tana mai cewa hakan barazana ce ga dimokuraɗiyya da zaman lafiyar yankin Yammacin Afirka.
A wata sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatar harkokin kasashen waje Kimiebi Ebienfa ya fitar a Alhamis din nan, gwamnatin ta ce ta samu labarin juyin mulkin kuma hakan na da matuƙar takaici da damuwa.
Sanarwar ta ce Nijeriya ba ta amince da wannan abu da ke ruguza da tsarin mulki da ci gaban dimokuraɗiyya ba, kuma ba iya a Guinea-Bissau kawai ba, har ma a yankin ECOWAS gaba ɗaya.
Gwamnatin ta ƙara da cewa wannan mataki ya karya ka’idar ECOWAS wanda ta yi kan dimokuraɗiyya da kyakkyawan mulki, tare da haramta karɓar mulki ta hanyar da ba ta dace ba.
