Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Nijeriya ta ɗage buɗe shafin neman aiki na Immigration, Civil Defence...

Gwamnatin Nijeriya ta ɗage buɗe shafin neman aiki na Immigration, Civil Defence da sauran hukumomi

Gwamnatin Nijeriya ta sanar da jinkirta buɗe shafin karɓar bayanan neman aiki na hukumar kula da shige da fice ta ƙasa (NIS), hukumar ba da tsaro ga fararen hula (NSCDC), hukumar kula da gidajen gyarin hali (NCoS) da kuma hukumar kashe gobara ta ƙasa (FFS).

Tun da farko, gwamnati ta bayyana cewa za a buɗe shafin ne ranar Litinin, 14 ga Yuli, 2025, amma yanzu ta jinkirta zuwa Litinin, 21 ga Yuli, 2025.

Sanarwar jinkirtawar ta fito ne daga ofisoshin da ke da alhakin gudanar da wannan aikin, inda suka ce matakin na ɗaya daga cikin shirye-shiryen tabbatar da tsari da inganci wajen gudanar da tantancewa da karɓar bayanan sabbin ma’aikata.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata