Ministan jin kai da rage talauci Bernard Doro, ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya da ke cikin mawuyacin hali cewa gwamnati tana da cikakken kudiri na taimaka musu da kuma tabbatar da tsaron rayukansu.
Yayin da yake zantawa da manema labarai a Jos a ranar Litinin, Doro ya ce manufar ma’aikatarsa ita ce tabbatar da cikar buri ga talakawa, masu gudun hijira, da sauran marasa galihu.
A cewarsa, ma’aikatar za ta inganta tsarin tallafi, fadada damar samun shirye-shiryen rage talauci, tare da tabbatar da cewa taimakon jin kai yana isa ga wadanda suka fi bukata.
Ministan ya kara da cewa gwamnati za ta aiwatar da ayyukan jin kai ba a matsayin taimako ba, sai a matsayin hakkin da gwamnati ke da shi ga ‘yan Nijeriya, domin tabbatar da abinci, ilimi, da mafaka ga marasa karfi.
