Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Sokoto za ta bude kofar tuba ga masu tayar da kayar...

Gwamnatin Sokoto za ta bude kofar tuba ga masu tayar da kayar baya dake neman sulhu a jihar

Gwamnatin jihar Sokoto ta bayyana aniyar ta na tattaunawa da masu tada kayar baya da ke dauke da makamai wadanda suke shirye domun ajiye makamansu su rungumi sulhu.

A wata sanarwa da mai bai wa gwamnan jihar Ahmed Aliyu shawara kan harkokin tsaro, Kanar Ahmed Usman rtd ya fitar, ya ce jihar ta jaddada mahimmancin tattaunawa kan domin kawo karshen rashin tsaro.

Sanarwar ta ce Gwamnati ta lura cewa ta hanyar tattaunawa tare da tabbatar da cewa jihar a shirye ta ke don tattaunawa da masu tada kayar baya da ke da sha’awar mika wuya da sake komawa cikin al’umma cikin lumana.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata