Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiGwamnatin tarayya ta fito da tsarin da zai kawo karshen wahalar da...

Gwamnatin tarayya ta fito da tsarin da zai kawo karshen wahalar da ake sha wajen tantance lambar NIN 

Gwamnatin tarayya ta amince da wani sabon tsari da hukumar dake bayar da katin dan kasa za ta rika amfani da shi don saukaka tantance lambar NIN ta ‘yan Nijeriya.

Wata sanarwa da shugaban sashen hulɗa da jama’a na hukumar NIMC, Kayode Adegoke, ya fitar a yau Talata a birnin Lagos, ya ce fadar shugaban kasa ta bayar da umarnin cewa dukkanin ma’aikatu da hukumomin gwamnati su rika amfani da wannan sabon tsarin domin tabbatar da tsaro ga bayanan mutane.

Ya ce wannan mataki zai tallafawa aikace-aikacen NIMC wajen samar da ingantaccen tsarin shaidar dan kasa na yanar gizo ga ‘yan Nijeriya da mazauna ƙasar bisa doka, a cewar jaridar Punch.

Sabon tsarin wanda ake kira NINAuth, yana aiki ta shafin yanar gizo, da manhajojin wayar salula, ko tsarin API, domin haɗawa kai tsaye da rumbun bayanan NIMC wajen tantance lambar NIN ta ‘yan kasa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata