Gwamnatin tarayya ta shigar da kara kan Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan a kotun babban birnin tarayya bisa zargin bata suna da yada karya.
An danganta karar da hirarta da ta yi a shirin Politics Today na Channels TV a ranar 3 ga Afrilu, 2025, inda ta zargi Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da tsohon Gwamnan Kogi, Yahaya Bello, da shirin kawar da ita ta.
Gwamnati ta ce hakan ya sabawa Sashe na 391 na dokar manyan laifuka, Cap 89, kuma laifi ne mai hukunci a ƙarƙashin sashe na 392.
A cikin tuhumar, gwamnati ta ce Natasha ta bayyana cewa, “taron da Akpabio da Yahaya Bello suka yi a daren nan yana da nasaba da yunkurin kawar da ni.”
