Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiGwamnatin tarayya ta jaddada kudirinta na magance matsalar rashin tsaro da ke...

Gwamnatin tarayya ta jaddada kudirinta na magance matsalar rashin tsaro da ke addabar kasar

Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu, ya bayar da wannan tabbacin ne a ranar Talata a ziyarar da ya kai Makurdi, babban birnin jihar Benue, domin jajanta wa al’ummar jihar kan asarar rayukan da aka yi a baya-bayan nan.

Da yake zantawa da manema labarai, Ribadu ya bayyana cewa gwamnatin shugaba Tinubu ta gaji matsalar tsaro, wanda hakan ke zama babbar barazana ga zaman lafiyar kasa, amma duk da haka an fara shawo kan matsalar.

A cewarsa, matsalar rashin tsaro da kasar ke fuskanta ta faro ne kimanin shekaru 15 da suka gabata kuma ya jaddada cewa ba ta da nasaba da siyasa, addini ko kabilanci.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata