Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Tinubu ta kawo karshen shekaru 10 babu masu zuba jari a...

Gwamnatin Tinubu ta kawo karshen shekaru 10 babu masu zuba jari a bangaren man fetur – Heineken Lokpobiri

Ministan man fetur na Najeriya Heineken Lokpobiri, ya ce kafin zuwan gwamnatin shugaba Tinubu, Najeriya ta shafe tsawon shekaru 10 ba tare da samun masu zuba hannun jari a bangaren ba.

A cewar ministan, hakan ya jawo mummunan koma baya a bangaren, sai dai a halin yanzu gwamnatin ta fara daukar matakan jawo hankalin masu zuba jarin.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa ministan ya bayyana haka ne ta cikin wata sanarwa da hadimarsa Nneamaka Okafor ta fitar, inda ya ce zuwan gwamnatin Tinubu ta yi matukar bunkasa fannin na man fetur, tare kuma da jawo hankalin masu zuba jari daga sassa daban daban na duniya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata