Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Tinubu ta tafka kuskure wajen rabon muƙaman Jakadun Nijeriya - ADC

Gwamnatin Tinubu ta tafka kuskure wajen rabon muƙaman Jakadun Nijeriya – ADC

Jam’iyyar ADC mai adawa a Nijeriya ta soki gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan sanar da rabon mukaman jakadu zuwa ƙasashen waje, tana mai cewa matakin kuskure ne na diflomasiyya kuma wata alama ce ta rashin kwarewar gwamnati.

A cikin wata sanarwa da Mallam Bolaji Abdullahi, Sakataren Yaɗa Labarai na ƙasa na jam’iyyar, ya fitar, ADC ta ce sanar da mukaman jakadu kafin samun amincewar ƙasashen da za su karɓe su na iya jefa Nijeriya cikin kunyatar diflomasiyya.

Jam’iyyar ta bayyana cewa a ƙarƙashin yarjejeniyar Vienna kan hulɗar diflomasiyya, musamman sashe na 4, dole ne ƙasar da ke aikawa da jakada ta fara neman amincewar ƙasar da za ta karɓe shi kafin sanar da nadin a hukumance.

Ta ce sanar da nadin jakadu sannan a ce ana neman wannan amincewa yana nuna gwamnati ba ta fahimci muhimman ƙa’idojin diflomasiyya ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata