Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Tinubu za ta fito da shirin bunkasa gundumomi karkashin shirin sabuwar...

Gwamnatin Tinubu za ta fito da shirin bunkasa gundumomi karkashin shirin sabuwar Nijeriya

Majalisar tattalin arzikin Nijeriya ta amince da wani sabon tsari mai suna Renewed Hope Ward Development Programme (RHWDP) da zai mayar da hankali wajen bunkasa yankunan gundumomi 8,809 a fadin kasar.

Ministan tsare-tsaren kasafin kudi da tattalin arziki, Sanata Atiku Bagudu, ne ya gabatar da tsarin yayin taron NEC, inda ya bayyana cewa shirin zai karfafa tattalin arziki da nufin cimma burin samun habakar tattalin arziki har kashi 15 cikin 100 na yankunan kafin shekara ta 2030.

Ya ce a kowane gunduma za a tallafa wa a kalla mutane 1,000 da ke da aiki ko sana’a, yayin da manyan gundumomi mutane 2,000 za a karfafa wa.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata