Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Tinubu za ta kashe Naira biliyan biyu don sake gina gidajen...

Gwamnatin Tinubu za ta kashe Naira biliyan biyu don sake gina gidajen da ambaliyar ruwa ta lalata a Mokwa jihar Neja

Shugaba Bola Tinubu ya amince da fitar da naira biliyan biyu domin sake gina gidajen mutanen da ibtila’in ambaliyar ruwa ya shafa a garin Mokwa na jihar Neja cikin gaggawa.

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ziyarci wadanda abin ya shafa a garin Mokwa da ke karamar hukumar Mokwa a ranar Laraba.

Ya kuma ba da tabbacin gwamnatin tarayya za ta magance matsalolin da mutanen da ibtila’in ya rutsa da su cikin gaggawa.

Ya ce shugaba Tinubu ya umurce shi musamman da ya je Mokwa domin jajanta wa jama’a game da bala’in da ya afku a garin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata