Sunday, April 5, 2026
HomeSiyasaGwamnonin APC da za su kammala wa’adin mulkinsu na biyu: Shin su...

Gwamnonin APC da za su kammala wa’adin mulkinsu na biyu: Shin su wanene za su gaje su?

Yayin da aka fara buga kugen siyasa ke gabanin zabukan gama gari na 2027, ana kara mai da hankali kan gwamnonin da aka zaba karkashin jam’iyyar APC wadanda ba za su sake komawa mulki ba saboda sun cinye wa’adin mulkinsu na biyu kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanadar.

A wannan rahoto, gidan talabijin na TVC News ta hada ya yi nazari kan gwamnonin da ke dab da kammala wa’adin mulkinsu kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

Yayin da wasu daga cikinsu suka fara nuna goyon baya ga wadanda suke son su gaje su, wasu kuma na jiran umarnin shugabannin jam’iyya kafin su tsara yadda magajin zai kasance.

Babagana Umara Zulum

Farfesa Babagana Umara Zulum, shi ne Gwamnan jihar Borno, yana wa’adinsa na biyu tun daga ranar 29 ga Mayu 2023 karkashin jam’iyyar APC.
An haife shi a ranar 25 ga Agusta 1969 a karamar hukumar Mafa ta jihar Borno, inda yake da digirin B.Eng daga jami’ar Maiduguri, da M.Sc daga jami’ar Ibadan, da kuma digirin digirgir a fannin Soil and Water Engineering.
Ya yi suna a aikin gwamnati da bangaren ilimi, inda ya kai matsayin Farfesa kuma ya taba zama Rector na Ramat Polytechnic.
Gwamna Zulum ya shiga siyasa a 2015 a matsayin kwamishinan farko na sake gina yankunan da rikici ya shafa, kafin a zabe shi gwamna a 2019, sannan aka sake zabensa a 2023.

Ahmadu Umaru Fintiri

Dan siyasa ne a Nijeriya wanda a yanzu yake matsayin Gwamnan jihar Adamawa.
An haife shi a ranar 27 ga Oktoba 1967 a Gulak, karamar hukumar Madagali, inda ya yi karatun farko kafin ya samu digirin BA a Tarihi a 1992 da kuma takardar digiri na gaba a fannin manufofi da dabarun gudanarwa a 2004 daga jami’ar Maiduguri.
Fintiri ya fara siyasa a majalisar dokokin jihar Adamawa, inda ya rike mukamai daban-daban har ya zama kakakin majalisa.
A wannan lokaci, ya taba zama mukaddashin gwamna sau biyu a 2012 da 2014 bayan tsige Gwamna Murtala Nyako, wanda hakan ya kara masa kwarewa a siyasa.
An zabe shi gwamna a 2019 sannan aka sake zabensa a 2023 karkashin jam’iyyar PDP, inda ya yi fice wajen gina tituna da inganta ilimi.
A wani babban sauyin siyasa, Fintiri ya sauya sheka zuwa APC a ranar 27 ga Fabrairu 2026, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen daidaita jihar Adamawa da manufofin gwamnatin tarayya karkashin Shugaban kasa Bola Tinubu.
An karbe shi a hukumance cikin APC a watan Maris 2026, inda aka amince da shi a matsayin jagoran jam’iyyar a jihar Adamawa.

Mai Mala Buni

Mai Mala Buni, shi ne Gwamnan jihar Yobe, yana wa’adinsa na biyu kuma na karshe tun daga ranar 29 ga Mayu 2019, bayan sake zabensa a 2023 karkashin APC.
An haife shi a ranar 19 ga Nuwamba 1967 a Buni Yadi, jihar Yobe, inda yake da digiri a fannin International Relations daga Benin Republic, da kuma digiri na biyu daga jami’ar Leeds Beckett.
Kafin siyasa, ya yi kasuwanci a bangaren noma, mai da sufuri.
Ya fara siyasa a 1991 a matsayin kansila, sannan ya rike mukamai daban-daban har ya zama babban jigo a APC a matakin kasa.
Gwamnatinsa na mayar da hankali kan farfado da yankunan da rikici ya shafa da kuma ci gaban ababen more rayuwa.

Muhammadu Inuwa Yahaya
Muhammad Inuwa Yahaya, shi ne Gwamnan jihar Gombe, yana wa’adinsa na biyu kuma na karshe tun daga ranar 29 ga Mayu 2019, bayan sake zabensa a 2023 karkashin APC.
An haife shi a ranar 9 ga Oktoba 1961 a Gombe, inda yake da digiri a Accounting daga jami’ar Ahmadu Bello, Zariya.
Ya fara aiki a bangaren gwamnati kafin ya koma kasuwanci, sannan ya taba zama kwamishinan kudi daga 2003 zuwa 2010.
Gwamnatinsa na tafiya karkashin tsarin DEVAGOM.
Kasafin kudin 2026 na Naira biliyan 617.95 ya ware kusan kashi 70 cikin 100 domin ayyukan ci gaba kamar hanyoyi, wuta, tsaro da noma.

AbdulRahman AbdulRazaq
AbdulRahman AbdulRazaq dan kasuwa ne kuma dan siyasa, yana wa’adinsa na biyu a matsayin Gwamnan jihar Kwara, kuma shi ne shugaban kungiyar gwamnonin Nijeriya (NGF).
An haife shi a ranar 5 ga Fabrairu 1960 a Zariya, jihar Kaduna, cikin gidan fitaccen lauya na farko a Arewacin Nijeriya.
Ya yi karatu a Kaduna da Ilorin, sannan ya samu horo a jami’ar Oxford da ke Ingila.
Kafin siyasa, ya yi fice a harkar mai da gas, inda ya kafa kamfanin NOPA Oil Services.
Ya shahara a siyasa bayan nasarar da ya samu a zaben 2019, inda ya kawo karshen tasirin siyasar Saraki a jihar Kwara karkashin tafiyar “Otoge”.

Babajide Sanwo-Olu
Babajide Olusola Sanwo-Olu dan siyasa ne, wanda ya zama Gwamnan jihar Lagos tun daga 29 ga Mayu 2019, kuma aka sake zabensa a 2023 karkashin APC.
An haife shi a ranar 25 ga Yuni 1965 a Lagos.
Ya yi karatu a jami’ar Lagos inda ya samu digiri da MBA, sannan ya samu karin horo daga cibiyoyi daban-daban na duniya.
Kafin siyasa, ya yi aiki a bankuna da kamfanoni masu zaman kansu.
Ya rike mukamai da dama a gwamnatin jihar Lagos kafin ya zama gwamna.
Mulkinsa na tafiya karkashin tsarin THEMES da ke mayar da hankali kan sufuri, lafiya, ilimi, tsaro da tattalin arziki.

Dapo Abiodun
Prince Dapo Abiodun, shi ne Gwamnan jihar Ogun tun daga 29 ga Mayu 2019, kuma yana wa’adinsa na biyu bayan sake zabensa a 2023 karkashin APC.
An haife shi a ranar 29 ga Mayu 1960 a Ogun.
Ya yi karatu a Amurka a fannin Accounting, sannan ya yi aiki a bangaren mai da gas.
Ya kafa kamfanoni kuma ya rike mukamai daban-daban na gwamnati.
Mulkinsa na karkashin tsarin ISEYA wanda ya hada da gine-gine, walwala, ilimi, matasa da noma.

Douye Diri
Sanata Douye Diri shi ne Gwamnan jihar Bayelsa, yana wa’adinsa na biyu.
An haife shi a ranar 4 ga Yuni 1959.
Ya fara aiki a matsayin malami kafin shiga siyasa inda ya rike mukamai da dama ciki har da dan majalisa da sanata.
Gwamnatinsa na mayar da hankali kan gine-gine, noma da tsaro.
A 2026, ya sanya hannu kan kasafin kudin Naira tiriliyan 1.01 domin ayyukan ci gaba.

Hope Uzodinma
Sanata Hope Uzodinma, shi ne Gwamnan jihar Imo, yana wa’adinsa na biyu kuma na karshe tun bayan sake zabensa a 2023.
An haife shi a ranar 12 ga Disamba 1958.
Ya yi kasuwanci a bangaren mai da gas kafin shiga siyasa, inda ya taba zama sanata.
Ya zama gwamna a 2020 bayan hukuncin kotun koli.
Mulkinsa na karkashin tsarin “3R” wanda ke nufin sake gina, gyara da farfado da jihar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata