Wani lauya kuma ɗan gwagwarmayar kare haƙƙin bil’adama, Deji Adeyanju, ya ce gwamnonin jihohi ba su da ikon doka na bayar da afuwa ko amnesty ga ’yan ta’adda, yana mai jaddada cewa hakan ya saɓa wa Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya.
Adeyanju, wanda ke shugabantar kamfanin Deji Adeyanju and Partners a Abuja, ya bayyana hakan ne a wata sanarwa, yana sukar yadda wasu gwamnonin jihohi ke amfani da tattaunawa da amnesty a matsayin dabarun rage matsalar tsaro.
Ya ce a ƙarƙashin Sashe na 212 na Kundin Tsarin Mulki, ikon gwamna na yafewa laifi ya ta’allaka ne kawai kan laifukan da dokokin jiha suka ƙirƙira, yayin da ta’addanci laifi ne na tarayya da ke ƙarƙashin Dokar Hana Ta’addanci, wadda ke cikin jerin ikon tarayya kaɗai.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito Adeyanju ya ce Shugaban Ƙasa ne kaɗai, bisa Sashe na 175, ke da ikon doka na bayar da amnesty kan laifukan ta’addanci, yana mai cewa duk wata afuwa da gwamna ya bayar a irin wannan hali ba ta da inganci a doka.
Adeyanju ya ƙara da cewa shirin amnesty na yankin Niger Delta da gwamnatin tarayya ta aiwatar shi ne misalin da ya dace da kundin tsarin mulki, ba shirye-shiryen jihohi ba.
