Monday, April 6, 2026
HomeSiyasaGwamnonin Nijeriya ba za mu lamunci a soke hukumomin zabe na jihohi...

Gwamnonin Nijeriya ba za mu lamunci a soke hukumomin zabe na jihohi SIECs ba – A.A SULE

Gwamna Abdullahi Sule na Nasarawa ya ce gwamnoni ba za su goyi bayan soke Hukomomin Zabe na Jihohi (SIECs) ba, yana mai cewa kamata yayi a gyara su maimakon a rushe su.

Daily Trust ta ruwaito gwamna Sule na cewa matsalolin SIECs sun hada da tsoma baki a siyasa, karancin kudi da rashin amincewar jama’a, kalubalen da yace hatta hukumar INEC na fama da su.

Inda ya kara da cewa akwai bukatar rinjayar da siyasa da ke haddasa kiran a soke SIECs, yana mai fatan taron zai samar da mafita kuma gwamnoni za su goyi bayan shawarwari masu amfani.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata