Ministan yaɗa labarai da wayar da kan al’umma Mohammed Idris, ya bayyana cewa gyare gyaren tattalin arziki da shugaban Tinubu ya aiwatar sun ceto jihohi 27 daga durƙushewar tattalin arziki.
Ministan ya bayyana haka ne yayin da yake bayani kan tasirin manufofin gwamnatin Tarayya, yana jaddada cewa sauye-sauyen da aka yi sun taimaka matuƙa wajen daidaita kuɗaɗen jihohi wajen biyan albashi da aiwatar da ayyukan raya ƙasa.
A cewar Mohammed Idris, kafin aiwatar da waɗannan gyare-gyare, jihohi da dama na fuskantar matsanancin ƙalubalen kuɗi, amma matakan da gwamnatin Tinubu ta ɗauka karkashin shirin Renewed Hope Agenda sun kawo sauƙi tare da ƙara wa jihohi hanyoyin samun kuɗaɗen shiga.
