Monday, April 6, 2026
HomeSiyasaHadakar ADC yaudarar ‘yan Nijeriya take yi - in ji Datti Baba...

Hadakar ADC yaudarar ‘yan Nijeriya take yi – in ji Datti Baba Ahmed

Datti Baba-Ahmed, tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party a zaben 2023, ya bayyana cewa haɗakar adawa da aka kafa a ƙarƙashin jam’iyyar ADC ba gaskiya ba ce, kuma tana yaudarar ‘yan Najeriya da ikirarin ceto ƙasar daga halin da take ciki.

Baba-Ahmed ya bayyana haka ne a cikin shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels a ranar Juma’a, inda ya ce: “Suna yaudarar mu,” yana mai jaddada rashin amincewarsa da tsarin.

Ya tuna cewa shi ne ya tsaya tare da Peter Obi a matsayin mataimaki a zaben shugaban ƙasa na 2023, wanda tsohon gwamnan Legas, Bola Tinubu na jam’iyyar APC ya lashe zaben.

Sai dai a cikin wannan hirar, Baba-Ahmed ya bayyana cewa ya shirya sake zama ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa tare da Obi a zaben 2027 idan aka samu dama.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata