Monday, April 6, 2026
HomeSiyasaHadimin Sanata Ipinsagba ya yi murabus saboda albashin N20,000 da ake biyansa

Hadimin Sanata Ipinsagba ya yi murabus saboda albashin N20,000 da ake biyansa

Oluwatunbosun Awe, mataimaki na musamman ga Sanata Olajide Ipinsagba mai wakiltar yankin Ondo Arewa a Majalisar Dattawa, ya yi murabus daga mukaminsa bisa albashin N20,000 da ake biyansa a kowane wata.

Awe, wanda ke matsayin jami’in hulɗa da mazabu a gundumar Isowopo Ward 2, karamar hukumar Akoko North East ta jihar Ondo, ya bayyana murabus dinsa a cikin wata wasika da aka fitar a ranar Laraba.

Ya ce albashin bai dace da halin tattalin arzikin Najeriya a yanzu ba, musamman duba da sabon albashin ƙasa na N70,000 da aka amince da shi kwanan nan.

Ya bayyana cewa duk da roƙon da ya yi wa Sanata Ipinsagba kan a duba albashinsa, ba a ɗauki wani mataki ba, kodadai makusantan sanatan sun yi watsi da dalilan murabus din nasa, kamar yadda Jaridar Daily Trust ta tabbatar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata