Friday, April 10, 2026
HomeLabaraiHar yanzu akwai damar samun ingantacciyar makoma a Najeriya - Goodluck Jonathan

Har yanzu akwai damar samun ingantacciyar makoma a Najeriya – Goodluck Jonathan

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya bukaci ‘yan kasar su ci gaba da jajircewa tare da hakuri, yana mai cewa kada su yanke kauna da samun ingantacciyar makoma.

Jonathan ya yi wannan kalami ne cikin sakonsa na taya Najeriya murnar cika shekaru 65 da samun ‘yancin kai, wanda hadiminsa Okechukwu Eze ya fitar a Abuja, kamar yadda jaridar punch ta ruwaito.

A cewar tsohon shugaban, tabbas akwai tarin kalubale da ke a gaban Najeriya, amma kada hakan ya sa gwiwar ‘yan kasa ta yi sanyi, domin kuwa akwai tarin damarmaki na samun sauyi mai kyau a nan gaba.

Ya kara da bukatar su kasance masu kishin kasa a kowane lokaci.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata