Sunday, April 5, 2026
HomeSiyasaHar yanzu gigin hana El-Rufai muƙamin minista bai sake shi ba -...

Har yanzu gigin hana El-Rufai muƙamin minista bai sake shi ba – Martanin APC ga kalaman El’rufai

Jam’iyyar APC ta soki kalaman tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, inda ta ce cike suke da rashin gaskiya da ruɗani.

Felix Morka, mai magana da yawun jam’iyyar, ya bayyana hakan a wata sanarwa, yana mai cewa El-Rufai na ci gaba da nuna bacin ransa kan gazawarsa ta zama minista, yana amfani da harshen batanci domin ɓata wa gwamnatin Tinubu suna.

Jigon a jam’iyyar haɗaka ta ADC ya ce sake zaben Shugaba Tinubu tamkar rushe sauran haɗin kan Nijeriya ne.

A cewar APC, El-Rufai da abokan tafiyarsa a jam’iyyar ADC ba su da wata manufa sai girman kai da kishin kansu, kuma ba su da wata hanya ko shiri da zai fi nasarorin da gwamnatin Tinubu ke samu a yanzu, kamar yadda ake gani a fannin noma, wutar lantarki, fitar danyen mai, gina hanyoyi, sauƙin hauhawar farashi da tallafin karatu na NELFUND.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata