Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiHar yanzu ina ckin jam’iyyar Labour, duk da na shiga hadaka –...

Har yanzu ina ckin jam’iyyar Labour, duk da na shiga hadaka – Peter Obi

Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour a zaɓen 2023, Peter Obi, ya bayyana cewa har yanzu yana cikin jam’iyyarsa ta LP, duk da kasancewarsa cikin sabuwar hadakar ’yan adawa da ke shirin kalubalantar Tinubu a zaɓen 2027.

Obi ya ce bai sauya sheƙa daga jam’iyyar Labour zuwa jam’iyyar ADC ba, wacce aka zaɓa a matsayin dandalin haɗakar ’yan adawa.

Ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen ɗan takarar gwamnan jam’iyyar Labour a jihar Anambra, Dr George Moghalu, da mataimakiyarsa, Lady Ifeoma Okaro, domin zaɓen gwamna da za a gudanar ranar 8 ga Nuwamba, 2025.

Peter Obi ya ƙara da cewa dukkan mambobin jam’iyyar Labour, har da ’yan majalisar tarayya da aka zaɓa, suna cikin wannan hadin gwiwa ta ’yan adawa.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata