Monday, April 6, 2026
HomeSiyasaHar yanzu INEC ba ta tabbatar da shugabannin mu na jihohi ba...

Har yanzu INEC ba ta tabbatar da shugabannin mu na jihohi ba – ADC

Jam’iyyar hadaka ta ADC ta bayyana cewa har zuwa wannan lokaci hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC ba ta tabbatar tare da sakin jerin sunayen shugabanninta a jihohi ba, sabanin yadda wasu rahotanni ke nunawa.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar Bolaji Abdullahi ya fitar a shafinsa na X, ya ce babu wata sanarwa game da batun daga INEC a hukumance ko kuma akasin haka.

Bolaji ya bukaci a yi watsi da rahotannin da ya bayyana a matsayin yunkurin kawo rudani a cikin jam’iyyar su ta ADC, kamar yadda jaridar punch ta ruwaito.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata