Tuesday, April 7, 2026
HomeLabaraiHare-hare kan ofisoshin ‘yan sanda ya yi sanadin halaka jami’an 'yan sanda...

Hare-hare kan ofisoshin ‘yan sanda ya yi sanadin halaka jami’an ‘yan sanda 45 a cikin shekara guda – Daily Trust

Wani rahoto ya bayyana cewa halin tsaro a Nijeriya ya ƙara tabarbarewa a cikin shekara guda da ta gabata, sakamakon hare-hare da aka rika kai wa ofisoshin ‘yan sanda, wuraren bincike a jihohi daban-daban na ƙasar.

Wadannan hare-hare sun yi sanadin halaka jami’an ‘yan sanda da dama, inda aka kona ofisoshi, aka kwace makamai, aka saki wadanda ake tsare da su.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa akalla jami’an ‘yan sanda 45 ne suka rasa rayukansu a cikin shekara guda sakamakon hare-hare kan ofisoshin ‘yan sanda, wuraren bincike da a jihohi da dama ciki har da Borno, Kwara, Enugu, Kano, Jigawa, Bauchi, Plateau, Kogi, Taraba, Benue, Zamfara, Niger, Edo, Kaduna da Oyo.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata